Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari
Kotun shari'ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari'a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.
Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.
Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.