Magigayi Abdulwahab wanda kuka fi sani da Awarwya rasu ne ayau Litinin.
Matashin jarumin dai ya rasu ne bayan yayi fama da rashin lafiya.
Mujallar matashiya ta ruwaito cewa, Ζan wasan Hausan ya rasu yayin da ake ci gaba da jimamin rasuwar Kamal Aboki wanda shima ya rasu sakamakon hatsarin mota akan hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Shi dai Awarwasa Ιan jihar Kano ne kuma ya fito a fina-finai da dama.
Daga cikin fina-finan da ya fi shahara, akwai; “A Duniya”, shirin mai dogon zango.
Allah ya jikansa darahama