Labarin Gida Me Abin Al'ajabii

Gidan mutuwa (House of Death) Wannan gida da kuke gani a hoto ana kiran gidan da suna "House of Death", Ma'ana "Gidan Mutuwa", yana wani gari ne mai suna; "Amaigbo Umu-Anu" a cikin jihar Imo. Mutanen kauyen basu san wanda ya gina gidan ba, haka kuma basu san mai rayuwa a gidan ba, sannan dare na yi za a ga hasken wutar NEPA ta ko'ina duk da cewa babu wata waya da ta sauka zuwa cikin gidan, haka ma ba a jin wani kara na generator. Abin da ya fi bada tsoro shine, babu wata kofa ta shiga gidan balle gate, duka gidan yana zagaye ne da Katanga. A shekarar 2012 wani matashi mai suna Ebuka Ikechwu ya yi yunkurin sanin menene ke rayuwa a cikin gidan, nan take ya yi tsalle ya haura katangar gidan, ganin shi (yaron) da a sake yi ba kenan har yau dinnan. Haka koda tsuntsuwa ba ta bi ta saman gidan. A shekara 2010 hukumar sauka da tashin jiragen sama ta jihar Imo mai suna "Imo state aviation center" ta haramtawa jiragen bi ta saman gidan. Idan kuka lura da kyau zaku ga kaya/tufafi an shanya su, wadannan kaya/tufafi suna canza kala lokaci bayan lokaci.
An tabbatar da cewa 2005 an hangi wata mata mai dauke da juna biyu a gefen taga (window) tana kuka fuskarta da jikinta duk jini, daga karshe ta kulle tagar (window) tun ranar ba a san yadda ta karke ba. Haka ma a shekarar 2018 wasu yara suna kwallo/tamaula sai ta fada gidan, nan da nan aka bugo kwallon daga cikin gidan ta dawo musu, shi kuma yaron da ya buga kwallon ta fada gidan a wannan ranan da tsakar dare ya mutu. Kafin ya mutu iyayen yaron suka ce sun ji an kwankwasa masu kofa sau uku, sai suka ji murya aka ce musu yaron ake bukata. Wannan gidan (House Of Death) yana Amaigbo a Umu-Anu kusa da school of health Imo state. Meson karin bayani zai iya zuwa ya samomana.
Previous Post Next Post