Matashi a garin Kudan ya yima tsunsunshi Jana'iza bisani bayan mutuwar tsuntsun.
Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.
“Wani matashi mai Suna Abubakar Ibrahim haifaffen garin Kudan Jihar Kaduna, ”inda aka wayi gari yayiwa wata tsunsuwarsa Jana'iza bayan mutuwarta."
Kamar yadda matashin ya wallafa hakan a babban Shafinsa dake yanar gizo, yace da darene wannan tsuntsun ya baƙunce shi har inda yake kasuwanci wato shagonshi, ba tare da yaga shihogowar tsuntsun ba, kwatsam ganinsa yayi.”
“Abubakar ya cigaba da bayar da labari turyan-turyan kan cewa kawai ya buɗe ido ne ya ga tsuntsun a saman kantan Shagonshi.”
Bugu da ƙari, Ganin wannan tsuntsun Sai ya sanya zukciyarshi ƙaunar tsuntsun, har ya Saba da tsuntsun, yaciga da ba tsuntsun kulawa dai-dai gwargwado iko.
“A kwan tashi rashin lafiya ya kama tsuntsun bisani yace ga garinku nan, gwargwadon faɗin Shi tashin a yayin zantawarshi da manema labarai.”
“Duba da Sabo da yayi da tsuntsun, matashi Abubakar yayiwa wannan tsuntsun Sutura kamar yadda ake yiwa mutum dazaran ya rasu haka har ƙabari inda ya bizne tsuntsun yana cike da alhinin mutuwarsa.”